1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen M23 sun yi wa mata fyade

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2023

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International, ta zargi mayakan 'yan tawayen kungiyar M23 da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da cin zarafin mata.

https://p.dw.com/p/4Neso
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango I 'Yan Tawaye | M23 | Mata
'Yan tawayen M23, sun ci zarafin mata fiye da 60 a KwangoHoto: Guerchom Ndebo/AFP

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasar Amnesty International, ta ce mata fiye da 60 ne suka fsukancin cin zarafin ta hanyar fyade, a yayin farmakin da kungiyar 'yan tawayen ta M23 ta kaddamar. Amnesty International ta bayyana cewa, ta samu hujjoji kan abin da ya farun daga shaidun da ta tattara a yankin. Tun karshen shekara ta 2021 mayakan M23 suke rike da yanki mai girma a Lardin Arewacin Kivu, inda fafatawa tsakaninsu da dakarun gwamnati ta janyo dubban mutane suka tsere daga gidajensu. Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuraddiyar Kwangon dai na zargin kasar Ruwanda mai makwabtaka da hannu kan tashe-tashen hankula wajen bai wa 'yan tawayen makamai, zargin da Ruwandan ta sha musantawa.