1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Waiwayen kalubalen 'yan jarida a Afirka

May 3, 2024

A yayin da ake ikirarin kara girka tsari na dimukuradiyya a cikin cin mafi yawan kasashen Afirka, dubbai na masu sana’a ta jarida na korafin sauke nauyi cikin wuya.

https://p.dw.com/p/4fUjz
Hoto: Mohamed Dahir/AFP/Getty Images

Can a takarda dai tarayyar Najeriya ta na sama a cikin 'yanci na taka rawar labarai a matakai daban daban cikin kasar. Kuma kama daga kundin tsarin mulki na kasar ya zuwa ga dokar 'yancin labarai masu mulki na Najeriyar sun yi tanadin rawa mai inganci ga sana'ar ta jarida a lokaci mai nisa.

To sai dai kuma a zahiri, dubban masu sana'ar ta jarida na fadar daya a kokari na sauke nauyin neman mulki na gari a matakai daban daban cikin kasar. An dai daure da yawa, an buge wasu a yayin kuma da aka kai wasu har ga kiyama duka a kokari na neman gyara bisa tattali na arziki da siyasar da ke kasar.

Nigeria I Journalist im Internet bei Arise News in Ikoyi
Dan jarida a NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Kuma duk da cewar dai kungiyar masu jaridar ta na-gari na-kowa ta daga kasar daga mataki na 129 zuwa 123 cikin 'yancin na jarida a shekarar bana, har yanzu da sauran tafiya a tsakanin aikin da tabbatar da 'yancin da ke da tasiri a cikinsa.

Ko ma ya zuwa ina ake shirin a kai cikin neman ingantar aikin, masu jaridar dai na kuma kallon rikicin iri iri daga jami'an tsaro da ma 'yan mulki a matakai daban daban cikin kasar.

Haruna Mohammed dai dan jarida ne da ke yi wa kafar Wikki Times aiki can a jihar Bauchi, kuma ya ce da kyar da gumin goshi suke iya aiyuka na wayar da kan mutane na garin.

World Press Freedom Day | Haiti 2002
Gangamin 'yan jarida a HaitiHoto: Thony Belizaire/AFP/epa/dpa/picture-alliance

Kokari na tsage gaskiya ko kuma rawa irin ta matan datsa dai, ana kuma zargin wasu a cikin masu sana'ar ta jarida da komawa amshi irin na shatan waka ga masu siyasa da masu fada ana ta amshi ko ba dadin.

Dr Kabir Lawanti dai na koyar da sana'ar ta jarida a jami'ar Ahmadu Bello da ke a Zaria, kuma ya ce Najeriyar na fuskantar masu aikin na jarida har iri biyu.

Pakistan | Demonstration zum Welttag der Pressefreiheit in Islamabad
Bukin ranar 'yancin 'yan jarida a IslamabadHoto: Farooq Naeem/AFP/Getty Images

Miliyoyi na 'yan kasar dai na kallon aikin na jarida kafa ta tabbatar da kaiwa ya zuwa inganta ta rayuwa da makoma cikin Najeriyar da ta share shekaru dai dai har 25 da sake girka tsari na siyasa, amma kuma har yanzu ke zaman jiran shan romonta.