1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maganin yaki da cutar Malaria

Abdullahi Tanko Bala
April 30, 2021

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi a kan samun nasarar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na Malaria da sabon maganin RTS, S.

https://p.dw.com/p/3soSU
Tansania  Ithani-Asheri Hospital in Arusha  Kind Malaria Test
Hoto: Katy Migiro/REUTERS

Jaridar ta ce shekaru biyar da suka wuce an sami gagarumar nasara a yaki da Malaria musamman a Afirka. Dalili shi ne tsarin nan na amfani da gidan sauro da aka yiwa feshin maganin sauron a 2016 inda kowane mutum guda yake amfani da shi.

To amma daga baya shirin ya sami tsaiko, hasali ma an sami koma baya a cewar hukumar lafiya ta duniya rabin alummar duniya na zaune cikin hadarin kamuwa da zazzabin Malaria. An yi kiyasin a 2019 mutane miliyan 229 suke dauke da cutar yayin da mutane dubu 409 suka rasu a sakamkon cutar. Yara yan kasa da shekaru biyar da suka kamu da cutar ke mutuwa a cikin kowane minti biyu.

Hukumar lafiya ta duniya na son ganin an yiwa kowane yaro allurar rigakafin da maganin RTS, S. inda aka fara a wasu kasashe uku na Afirka da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi. Allurar ta RTS, S wadda kamfanin hada magunguna na Glaxo smith Kline ya samar tare da hadin gwiwa da shirin samar da allurar rigakafin Malaria MVI za ta rage tasirin kwayar cutar Plasmodium. Kuma za a yi ta ne a matakai hudu ga yara yan watanni biyar zuwa watanni 17 da haihuwa.

Anopheles Moskito Malaria Überträger
SauroHoto: Soumyabrata Roy/NurPhoto/picture alliance

Hukumar lafiya ta duniya na fatan yanke shawara a kan ko ya kamata sauran kasashe su ma su yi amfani da allurar RTS, S din domin maganin cutar Malaria.

Zanga zangar adawa da juyin mulkin soji a Chadi ya jefa Faransa cikin halin tsaka mai wuya. Wannan shi ne take sharhin Jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Dubban jama'a sun amsa kiran jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula wajen zanga zangar da suka yi wa take Wakit Tama da ke nufin lokaci ya yi. Ko da yake Janar Mahamat jagoran mulkin sojin da ya gaji mahaifinsa Idriss Deby ya nada wani dan siyasa Albert Pahimi Padacke a matsayin Firaminista yan zanga zangar sun bukaci mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.

Jaridar ta ce bacin ran yan zanga zangar bai tsaya ga sojojin da suka yi juyin mulki kadai ba, sun fusata da kasar Faransa tsohuwar uwar gijiyar da ta yi wa kasar Chadi mulkin mallaka inda suke suka ga shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda suka sanya wa jan fenti a hotunansa. Masu zanga zaangar sun zargi Faransa da yin katsalandan a al'amuran cikin gida na kasar Chadi.

Tun shekarar 2013 sojojin Faransa suke yankin Sahel inda suke aikin kiyaye zaman lafiya a kasashen Mali da Mauritania da Burkina Faso da Niger da kuma Chadi. Yan zanga zangar dai sun baiyana halartar Macron wajen jana'izar Deby a matsayin nuna goyon baya ga juyin mulkin sojin. A yanzu dai kasancewar farar hula a cikin sabbin shugabannin kasar fatan da al'umma da kuma yan adawar ke yi shi ne ganin kafuwar dimukuradiyya da dorewarta a kasar Chadi. 

Tschad Armee FACT Rebellen Gefangene
'Yan tawayen ChadiHoto: Chadian Army/AFP

Ita kuwa Jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhinta mai taken shugaban Somalia ya nuna hasken janye tsawaita wa'adin mulkinsa.

Jaridar ta ce shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya gabatar da jawabi a daren ranar Talata, 'yan Somalia da dama sun yi tsammani shugaban wanda ke fuskantar kakkausar suka da rashin farin jini zai murabus. An yi ta zanga zanga a yan kwanakin da suka wuce a birnin Mogadishu da yunkurin kara wa kansa wa'adin mulki na shekaru biyu. Amirka da kungiyar tarayyar Turai sun yi barazanar kakaba masa takunkumi.

A yanzu dai ya sanar da majalisa cewa zai janye shirin karin shekaru biyu na wa'adin mulkinsa kuma zai gudanar da zabe nan ba da jimawa ba. Watakila wannan zai kwantar da hankula na dan wani lokaci amma matsaloli na nan kwance wadanda ba a warware su ba.

Jaridar ta ce yayin da sojoji ke kokarin shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke ciki a waje guda yan adawa na cigaba da fada da juna sannan a waje guda kuma  mayakan al Shabaab na kokarin yin amfani da damar gibin tsaro da aka samu wajen karbe ragamar iko).