1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen Cryptocurrency a Najeriya

February 9, 2021

Muhawara a Najeriya kan batun batattun kudi na zamani wato Crypptocurrency da gwamnati ta zarga da taka rawa a aikata laifuka da kuma masu ganin matakin na iya dakile kokarin kasar na koma wa ga zamani a harkokin kudi.

https://p.dw.com/p/3p80f
Bitcoin Illustration I Dollar USD Banknoten
Bitcoin: Fitaccen tsarin boyayyun kudi na zamani wato CryptocurrencyHoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture-alliance

Muhawarar dai ta barke ne kasa da 'yan sa'o'i da haramta cinikin batattun kudi na zamani wato Cryptocurrency a Tarayyar Najeriyar. Boyayyun  kudin na zamani ko kuma Cryptocurrency dai, na taka muhimmiyar rawa  a Najeriyar, kasar da ke zaman ta kan gaba a daukacin nahiyar Afirka ga batun mu'amalar kudin da ke dada daukar hankali cikin kasar.

Barazana ga tsaro?

To sai dai kuma karuwar barazana a cikin harkoki na kudi dai, ya tilasa babban bankin kasar na CBN sanar da sabuwar manufar haramta cinikin kudin na zamani cikin kasar. Bankin CBN dai ya ce ya kaddamar da bincike ga daukacin asusun ajiya na bankuna cikin kasar da ke harkar kudin na Cryptocurrency da nufin gano rawar da masu asusun ke takawa a harkar halasta kudi na haramun da ma damfara cikin harkokin kudi na duniya.

Facebook - Kryptowährung - LIBRA
LIBRA: Guda daga cikin hanyoyin cinikayyar boyayyun kudin zamani CryptocurrencyHoto: picture-alliance/U. Baumgarten

A bara kadai  dai Tarayyar Najeriyar ta yi hada-hadar da ta kai dalar Amirka miliyan 200 na boyayyun kudin na Cryptocurrency, kudin da ke kara farin jini musamman a tsakanin matasa na kudancin kasar da suke masa kallon damar arziki daga zaune, cikin kasar da aiki ke dada wahala. To sai dai kuma maimakon cinikin boyayye dai, sannu a hankali kudin sun koma dama ta damfara da boye kudin haramun da ma hanyar karbar kudin fansa ga 'yan bindiga.

Dakile hanyar cinikayya ta zamani

Dr Umar Ardo dai ya biya dalar Amirka dubu 15 ta kudin boyayyu ga barayi na mutane da nufin ceto 'yarsa da aka sace a Abuja shekaru biyu baya. Barazana ga 'yan kasa ko kuma ciniki na zamani dai, majiyoyin babban bankin sun kira garkuwa da rumbun ajiya na bayanai na guda a cikin bankunan kasar, a matsayin daya daga cikin hujjojji na matakan da ke tada jijiyar wuya cikin Tarayyar Najeriyar a halin yanzu.
Kuma ko bayan nan dai Hukumar Kula da Manyan Laifuka ta Amirka FBI, ta sanarwa da bankin rawar da 'yan kasar da daman gaske suke takawa wajen boye kudin sata ta amfani da dabarar ta zamani. Tarrayar Najeriyar dai na cikin tsaka mai wuya, tsakanin tafiya zuwa ga zamani cikin harkoki na kudi da kuma kare miliyoyin 'ya'yanta da yanzu haka ke fuskantar barazana daga cinikin kudin.

Kryptowährung "Ether"
Ana iya amfani da Ether wajen cinikayyar boyayyun kudin zamani CryptocurrencyHoto: picture-alliance/NurPhoto/J. Arriens

Zaune kara zube?

To sai dai kuma a fadar Dakta Sirajo Yakubu da ke zaman kwararre cikin harkoki na kudi a jami'ar Baze da ke Abuja, Tarayyar Najeriyar na iya koyi da wasu kasashe na duniya da suka bai wa kudin matsayi na dabam. Sama da kamfanoni 80 ne dai a yanzu haka ke cikin cinikin boyayyun kudin na zamani, to sai dai kuma babu ko da guda daya da ke karkashin iko na hukumomin masu alhakin kula da harkokin kudi a Najeriyar.