1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHabasha

Habasha: Al'umma na kwana da yunwa

February 5, 2024

Matsalar fari da tashe-tashen hankula da cin-hanci da rashawa, kadan ne daga cikin dalilan da suka haddasa yunwa a kasar Habasha, matsalolin kuma da ta yiwu za a iya kauce musu.

https://p.dw.com/p/4c4n7
Italiya | Majalisar Dinkin Duniya | Hukumar Samar da Abinci | Karramawa |  Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy AhmedHoto: United Nations FAO 2024

Masana na fargabar cewa, shekaru 40 bayan annobar yunwa da aka fuskanta a Habasha a 1985 kasar na shirin sake fuskantar matsalar in har ba a gaggauta daukar mataki ba a cewar masana. Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane kimanin miliyan 20 ne suke bukatar taimakon abinci na gaggawa a kasar. Wata dattijuwa mai shekaru 65 da haihuwa daga yankin Atsbi a gabashin Tigray, ta shaida wa DW cewa sau biyu rak aka yi ruwan sama a yankin abin da tun da ta ke a rayuwarta ba ta taba ganin irin wannan yanayin ba.

Karin Bayani: Tigray na fafutukar samun zaman lafiya bayan yaki

Shugaban yankin Tigray da ke cikin wadi na tsaka mai wuya Getachew Reda ya fada a baya-bayan nan cewa, fiye da kaso 90 cikin 100 na al'ummar yankin suna fuskantar barazanar yunwa har ma da mutuwa. Hukumomin na Tigray sun yi gargadin cewa, halin da ake ciki a yankin ka iya kai wa makamancin yanayin da aka shiga a 1984 zuwa 1985 da ya hallaka dubban mutane. Sai dai da farai gwamnati a Addis Ababa ta yi kokarin kawar da rahotannin da cewa ba gaskiya ba ne, inda ta zargi  Reda da sanya siyasa cikin lamarin.

Habasha | Tigray | Getachew Reda | Yunwa
Shugaban yankin Ti´gray na Habasha Getachew RedaHoto: Million Haileselassie/DW

A shekarar 2022 wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya wallafa rahotons, inda ya zargi gwamnatin Habasha da yin amfani da dabarar azabtar da mutane da yunwa a matsayin makami abin da ke zaman take hakkin dan Adam da aka aikata a rikicin na Tigray. A bisa alkaluma na baya-bayan nan dai, kimanin mutane 372 ne suka rasu, sakamakon tsananin yunwa a cikin watanni shida da suka wuce a arewacin Habasha. Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa, sakamakon tabarbarewar tsaro da kuma yanayin siyasa da kalubale ta fuskar ayyukan noma ba a samu an noma gonaki masu yawa ba.

Karin Bayani: Tashin hankali na karuwa a yankin Amhara

A watan Maris na 2023 an dakatar da bayar da tallafin abinci saboda kamarin sace gudunmawar da ake bayarwa musmaman hatsi ,kamar yadda Laetitia Bader jami'ar kungiyar Kare Hakkin dan Adam a yankin Kahon Afirka ta nunar. Abin damuwa a yanzu shi ne, yunwa za ta zama sila ta hallaka kananan yara masu yawa a kasar. A yanzu dai firaministan Habasha Abiy Ahmed ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa kasar Italiya, inda Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba shi lambar yabo saboda kokarinsa na bunkasa noman alkama. Sai dai wannan a cewar Bader ta kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch, lamari ne mai daure kai a yanayin da kasar ta Habasha ke ciki na annobar yunwa a ce an ba shi wannan lambar yabo.