1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyya mai mulkin a Togo ta lashe zabe

May 5, 2024

Sakamakon wucin gadi na hukumar zaben kasar Togo ya nuna cewa jam'iyya mai mulki ta lashe zaben 'yan majalisun dokoki da na yankuna.

https://p.dw.com/p/4fW4q
Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe
Hoto: Ute Grabowsky/photothek/IMAGO

Sakamakon wucin gadi na zaben Togo ya nuna cewa jami'iyyar Shugaba Faure Gnassingbe ta UNIR ta lashe kujeru 108 cikin 113 na majalisar dokoki a zaben da kashi 60 cikin 100 na al'ummar kasar suka fito.

Ana dai ganin nasarar da jam'iyyar ta samu a zaben na ranar 29 ga watan Afrilun wannan shekarar ya biyo bayan amince wa da kwaskware kudin tsarin mulkin kasar da 'yan majalisu masu barin gado suka yi a farkon wannan shekarar.

Karin bayani: An saka ranar zabukan Togo da aka dage bayan rudanin siyasa

Masu sukar lamirin gwamnatin kasar na ganin sabuwar dokar da za ta bai wa 'yan majalisa damar nada shugaban kasa zai kara tsawaita wa'adin mulkin Shugaba Gnassingbe ne na tsawon shekaru 19.

Shugaban ya dare kan madafun ikon kasar Togo ne tun a shekarar 2005 bayan da ya gaji mahaifinsa, Shugaba Eyadema Gnassingbe da shi ma ya mulki kasar na tsawon shekaru 38.