BATUTUWA
Bajamushe a Wurin Aikinsa
Ku koyi sanin Jamus ta hanyar rayuwar al´ummomin dake zaune a sassa daban-daban na ƙasar.
Deutsche Welle ta tura wakilai kowane lungu, da kowane saƙo na ƙasar Jamus, domin tattaunawa da ma´aikata.
Kudu da arewa, gabas da yamma, ma´aikata na ba da labarin rayuwarsu ta yau da kullum, da kuma bururukan dake cikin zukatansu. Tare da waɗannan rahotanni masu taken „Gesichter Deutschlands“ ko "Bajamushe a Wurin Aikinsa" za ku ji bayanai daga tushe, game da yanayin aiki a Jamus da suffofin rayuwar Bajamushe. Za ku iya sauraron rahotanni na harshen Hausa a cikin shirye-shiryenmu na yamma kowace Talata da Alhamis. Sannan za ku iya karanta labarin da harsunan Faransanci da Turanci a cikin wannan shafi.