1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages

 
 
 

 

News | 09.01.2009 | 19:00 UTC

Sabon faɗa ya ɓarke a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo

 Rahotanni daga Jamhuriyar Demokraɗiyar Kongo sun ce wani sabon faɗa ya ɓarke tsakanin 'yan tawaye da sojojin sa kai dake goyon bayan gwamnati a gabashin ƙasar, yayin da jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya(MDD)  ke ganawa da shugaban 'yan tawaye Laurent Nkunda.  Wani jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya faɗawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan tawayen da sojojin sa kai na Mai-Mai sun yi musayar wuta a kusa da birnin Goma.Tun farko a yau Juma'a jakadan majalisar na musamman Chief Olusegun Obasanjo ya gana da Nkunda kan batun ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a ƙasar,ya kuma gana da shugabannin Kongo da Ruanda inda ya baiyana imanin cewa za a samu zaman lafiya tsakanin ɓangarori da ke rikici a yankin.


More news | 09.01.2009 | 19:00 UTC

News overviewPrint all news itemsPrint



 
Picture of the Day
ImageOfTheDay

DW-TV EUROPE live

euromaxx (deutsch) - Rammstein im deutschen Chor-Repertoire